Majiyar muryar JMI ta nakalto Kanar Saifullahi Rasheed-Zade kwamandan runduna ta 8 , Najaf-Ashraf ta Esfahan yana fadar haka a daren jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa rundunar ta samu labari daga wajen mutanen gari kan sun ga wata mota wacce aka ajiye a wata unguwa a tsakiyar garin Najaf-Abad, wacce suke da shakku a kanta.
Rashid-Zade ya kara da cewa sashen kwance boma-boman na rundunar ta yi nasarar gano cewa akwai boma-bomai da aka ajye a cikin motar kuma da sami nasarar kwance su ba tare da wata asaraba. Ya ce Kwararru a fagen ayyukan kwance bom da farko sun dauki bom din zuwa bayan gari kafin su kwance shi.
Ministan mai kula da yansandan ciki na kasar Iran Sayyeed Mahmood Alawi ya bayyana a ranar 25 ga watan Yulin da ta gabata kan cewa jami'an tsaron kasar Iran sun sami nasarar kwance boma bomai da yan ta'adda suka dana a wurare daban daban a cikin kasar Iran hau sau 120 a cikin yan shekarun da suka gabata.288